An gano gawarwakin wasu yara a Australia

Australia
Image caption Lamarin ya auku ne kasa da mao guda bayan da wani dan bindiga ya yi garkuwa da wasu mutane a wani shagon shan shayi

'Yan sanda a kasar Australia sun ce sun gano gawawwakin wasu yara su takwas da aka kashe.

Kisan ya faru ne a wani gida dake birnin Cairn a arewacin yankin da ake kira Queensland.

Rahotanni sun ce dukkanin yaran da shekarunsu bai wuce uku zuwa hudu ba an daba musu wuka ne.

Rahotanni sun ce an kai wata mata asibiti itama dauke da raunuka dake da alamun na wuka ne.