'Fursunoni na da 'yancin kada kuri'a a Nigeria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun ta ce INEC ta tabbatar fursunonin sun kada kuri'unsu

Wata babbar kotu a Nigeria ta ce fursunoni na da 'yancin kada kuri'a a dukkanin zabuka a kasar.

Alkalin kotun ta Enugu, Mohammed Lima ya yanke hukuncin cewa duk wani fursuna da shekarunsa suka kai 18 zai iya kada kuri'a.

Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban hukumar zabe, Mr. Kayode Edowu ya shaida wa BBC cewa za su yi nazari kan hukuncin kotun tukuna.

Inda ya kara da cewa a iya sanin hukumar zaben babu rumfunar zabe a gidajen kurkuku.