Ma'aikatan mai sun janye yajin aiki a Nigeria

Image caption Fannin mai ne ke samar da kashi mafi tsoka na kudaden shigar Najeriya

Manyan kungiyoyin kwadago na ma'aikatan mai da iskar gas a Najeriya, PENGASSAN da NUPENG sun janye yajin aiki da suka shiga a wannan mako.

Hakan ya biyo bayan jerin tattaunawa da shugabannin kungiyoyin suka yi da bangaren gwamnati.

Yajin aikin ya janyo dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai, yayin da ake gab da fara shagulgulan kiristimeti.

Kungiyoyin sun shiga yajin aikin ne saboda wasu bukatu kamar neman gwamnati ta inganta fannin mai da kuma amincewa da kudurin dokar garambawul a fannin da ke jan kafa a majalisa.