Ban Ki-Moon na ziyara a yammacin Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon na cigaba da ziyara a kasashen da ke fama da cutar Ebola.

Ya ziyarci Guinea, kuma ana saran zai je Mali a yau kafun yaje Ghana inda Majalisar Dinkin Duniyar keda cibiyar yaki da cutar.

A jiya juma'a, Ban Ki-Moon ya jinjina wa jama'ian Majalisar, musaman ma wadanda cutar ta hallaka, a bisa sadaukar da kansu da suka yi wajen yaki da ita.

Mr Ban ya kuma yi alkawarin cewa Majalisar zata cigaba da taimakon da ta ke yi wajen yaki da cutar.

Yace: "kamata yayi ace ganin bayan cutar kwata-kwata ya zama burin kowa da kowa".

Sama da mutane dubu bakwai ne citutar ta hallaka a kasashen yammacin Afrika.