Liberia na zabe duk da fargabar Ebola

Masu zabe a Monrovia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zabe a Monrovia

Yan takarar da ke fafatawa a zaben sun hada da tsohon dan wasan kwallon kafar nan George Weah da kuma Robert Sirleaf dan shugabar kasar ta yanzu wadanda ke fafatawa ta neman kujerar majalisar dattijan ta gundumar Monrovia.

A waje guda dai hukumomin lafiya sun kai jami'ai da kuma naurar auna zafin jikin dan Adam a mazabu a fadin kasar.

Mataimakin Ministan lafiya na kasar Tolbert Nyenswah wanda ke jagorantar yaki da cutar ebola a Liberia yace duk mai kada kuri'ar da aka samu zafin jikinsa ya haura maki 37 a maunin Celcius za'a janye shi daga kan layi domin kai shi cibiyar kula da lafiya ta musammman don kara duba lafiyarsa.

Yace lafiyar jama'a a lokacin yakin neman zabe da kada kuri'a yana da muhimmanci sosai.

Mr Nyenswah yace babban abin farin ciki shine yadda ake samun raguwar masu cutar a cibiyar kula da masu ebolar a Liberia yana mai cewa a kullum cutar raguwa take.

Karin bayani