An gano sansanin Boko Haram a Kamaru

Cameroon Hakkin mallakar hoto
Image caption Wannan shine karon farko da aka taba samun irin wannan sansani

Gwamnatin Kamaru ta ce ta gano wani sansanin da ake horar da matasa wanda 'yan Boko Haram suka kafa a garin Guirvidig da ke Lardin arewa mai nisa.

Wannan shi ne karon farko da hakan ya bayyana a idon jami'an tsaro.

Bayanai sun nuna cewa a yanzu haka matasan da kuma malamansu na hannun jami'an tsaro na Jandarma a birnin Maroua inda ake gudanar da bincike a kansu.

Hakan ya biyo bayan hadin kan da jama'a suka bai wa jami'an tsaro ne a ire-iren ayyukan binciken da suke yi.