"Kasashe masu tasowa na asarar tiriliyan daya a shekara"

Nigeria Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Najeriya na daga cikin kasashen da wannan matsala ta yi kamari in ji kungiyar

Wani bincike da wata Kungiya mai sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin kudi a duniya ta ce kasashe masu tasowa na asara tiriliyan daya a duk shekara.

Kungiyar mai suna Global Financial Integrity dake da shelkwata a Amurka ta ce ana asarar kudaden ne ta hanyar halatta kudaden haram.

Nijeriya dai na daya daga cikin kasashen da matsalar ta fi kamari a cewar binciken da aka fitar a makon jiya.

Masu sharhi da dama sun bayyana cewa lamarin yana karya tattalin arzikin kasa da kuma hana samar da ababan more rayuwa ga jama'a.