Direba ya kutsa kai cikin jama'a da mota a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Faransa na cewa wani mutum dake yin kabbara ya kutsa kai da mota kan titin da jama'a ke tafiya a kasa a birnin Dijon.

An ruwaito cewa mutane 11 sun jikkata, biyu daga cikinsu sun sami munanan raukuna.

Wsau rahotannin sun ce akwai fasinjoji biyu a cikin motar mutumin.

A ranar asabar 'yan sandan Faransa sun harbe wani mutum har lahira da shima yake yin kabbarar yayinda ya kai hari kan jami'an 'yan sanda uku a wani ofishin 'yan sanda dake tsakiyar birnin Joue-les-Tours