Kura ta lafa a garin Geidam na Yobe

Hakkin mallakar hoto yobe govt
Image caption Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin dake fuskantar hare haren 'yan Boko Haram

Wasu majiyoyi a jihar Yobe a Najeriya, sun shaidawa BBC cewa kura ta lafa a garin Geidam na Jihar Yobe bayan da wasu 'yan Bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai hari akan garin da yammacin lahadi

Mazauna garin sun ce sun ji karar harbe-harbe da tashin bama-bamai kuma yawancin su sun tsere.

Wannan harin dai na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan harin da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai a garin Damagun na jihar Yoben.

Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohin arewa maso gabas dake fama da hare haren 'yan kungiyar Boko Haram.