An harbe 'yan sanda 2 a New York har lahira

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda a birnin New York na fuskantar bincike

Rahotanni daga birnin New York na Amurka, na cewa wani mutum da ya rubuta sakon nuna kin jin 'yan sanda a dandalin sada zumunta da musayar ra'ayi, ya harbe wasu 'yan sanda biyu har lahira, sannan daga baya shima ya harbe kansa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bill Bratton, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce mutumin ya harbe 'yan sandan ne yayin da suke zaune a cikin motarsu, kuma saboda suna sanye ne da kayan 'yan sanda.

Magajin Garin na New York, Bill de Blasio, ya ce duk wanda ya ga an saka wani sako dake nuna barazana ga 'yan sanda a dandalin sada zumunta, to ya yi maza ya sanar da hukuma.

Kisan 'yan sandan na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a da dama ke ke ci gaba da nuna fushinsu bisa kin hukunta 'yan sanda fararen fata dake kashe bakaken fatan da basa dauke da makamai.