Za mu fitar da fim din Shugaban Korea- Sony

Sony Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Sony ya ce yana kan bakarsa ta fitar da fim din

Kamfanin Sony Picture mai shirya fina-finai ya ce yana duba hanyoyi da dama da zai fitar da fim dinsa akan shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un.

A baya kamfanin ya soke wannan yunkuri bayan da aka zargi Korea ta Arewar da satar bayanan kamfanin.

Yanzu haka rahotanni na cewa shugaba Barack Obama wanda ya ce kamafnin Sony yay yi kuskure da ya soke fitar da fim ya sha alwashin cewa Amurka za ta maida martani ga kasar ta Korea kan wannan kutse.

A ranar juma'ar da ta gabata ne hukumomin Amurkan suka danganta Korea da kutsen wanda ya fitar da bayanai masu muhimmanci a baina jama'a.

Hakan ya sa kamfanin na Sony ya janye shirin bayan barazana da ya samu.

" Za mu maida martani" Obama ya bayyanawa manema labarai a ranar juma'a da ta gabata ba tare da ya bayyana matakin da Amurkan za ta dauka ba.

Ya kuma kara da cewa "ba za mu amincewa wani dake waje ya dinga tace mana finafinanmu ba."

A cewar Mr. Obama ya na da matukar muhimmanci kudin adana bayanai na hukuma da ma na jama'a su kasance a tsare saboda muhimmancinsu ga tattalin arziki da rayuwa ta yau da kullum.