An rufe runfunan zabe a kasar Tunisia

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar ta Tunisia ta kama hanyar kafa wani sabon tarihi a wanzuwar ta na kasa.

Dukkan wanda ya sami nasarar lashe wannan zagaye na biyu na zaben shine zai kasance shugaba na farko da jama'a suka zaba bisa tafarkin dimokradiyya a daukacin kasashen larabawa.

Jami'ai sun ce zaben ya tafi lami lafiya, kuma ya samu halartar masu sa ido daga kasashe daban, daban.

'Yan takarar biyu dai su ne shugaban kasar na wucin gadi, Moncef Marzouki da kuma Beji Ciad Essebsi mai shekaru 88, wanda ya samu kuri'u mafi yawa a zagayen farko.

An baza jami'an tsaro sosai bayan da masu tada kayar baya suka yi kokarin kawo hargitsi.