Ana zaben shugaban kasa a Tunisia

Hakkin mallakar hoto EPA

Masu kada kuri'a a Tunisia za su zabi sabon Shugaban Kasar a yau.

Wanda ya yi nasara shi ne zai kasance shugaban kasa na farko da aka zaba a tarihin kasar.

Shekaru hudu bayan boren da ya janyo hanbarar da Zine Abedine Ben Ali da kuma tunzura irin wannan bore a daukacin kasashen larabawa, Tunisia ita ce kawai kasar da ta sami nasarar komawa tsari irin na demokradiya.

A zagaye na biyu na zaben, shugaba mai ci Moncef Marzouki, wani mai fafutukar kare hakkin dan adam da yake da farin jini wajen talakawan kasar na fuskantar hamayya daga Beji Caid Essebsi wanda yake da goyan baya mai karfi a lardunan kasar masu arziki.

A zagayen farko na zaben Mr. Essebsi ne ya lashe mafiyawancin kuri'un da aka kada.