Gombe: Bam ya kashe mutane 20 a tasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin da aka kai a kasuwar Terminus a Jos

Mutane a kalla 20 ne suka rasu sannan fiye da 40 suka jikkata sakamakon tashin bam a wata tashar mota a Gombe da ke arewacin Nigeria.

Kungiyar agaji ta Red Cross ce ta tabbatar wa BBC wannan adadin sakamakon fashewar bama-bamai biyu a tashar Dukku a Gombe.

Tashar Dukku tsohuwa ce mai cinkoson jama'a a cikin gari kuma ba a fadadata ba a zamanance.

Wannan ne hari na biyu a tasha motoci a jihar Gombe cikin watanni biyu, saboda a watan Oktoba ma an kashe mutane 10 a wani harin bam.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma kuma ana zargin Boko Haram wacce ke hallaka mutane a arewacin Nigeria, da yin wannan aika-aikar.

Jihar ta Gombe dai ta sha fuskantar hare-haren 'yan Boko Haram a baya bayan nan.