Ana bukatar kara azama don yakar Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dr. Tom Frieden na cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka

Daraktan cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka ya ce akwai bukatar a kara azama domin dakile yadda cutar Ebola ke cigaba da yaduwa a wasu kasashen yammacin Afrika.

Dr. Tom Frieden, ya sanar da hakan ne bayan ya kammala ziyarar da yakai karo na biyu a kasashen Laberiya, da Salio da Guinea masu fama da cutar Ebola.

Ya ce al'amuran da ya gani dangane da cutar a wani fannin suna da karfafa gwiwa, yayin da a wani fannin kuma, suke da tsoratarwa.

Daraktan ya ce abun ya na karfafa gwiwa idan aka yi lakari da yadda fafutukar yaki da cutar ta inganta a cikin watanni biyu da suka gabata.

Sai dai Dr. Frieden ya ce al'amarin yana da tsoratarwa idan aka yi dubi da yadda cutar Ebola ke cigaba da yaduwa ba kakkautawa a Saliyo, da kuma wasu sassan biranen Monrovia da Conakry.

Kimanin mutane dubu 7 da 533 ne cutar Ebola ta kashe tun bayan bullar ta bara a Guinea, inda ta yadu zuwa wasu kasashe.