Ebola: IMF na kawo cikas wajen yaki da cutar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar ebola ta halaka mutane sama da 7,000 a yammacin afirka

Masu bincike a Burtaniya sun ce akwai yuwuwar cewa wasu sauye sauye da hukumar ba da lamuni ta IMF ta yi, sun taimaka wajen yaduwar cutar Ebola a Yammacin Afrika.

Masu bincike wadanda suka fito daga jami'o'in Cambaridge da Oxford sun ce wasu tsare-tsare hukumar ta IMF, sun durkusar da bangaren kiwon lafiyan kasashen Saliyo da Guine da kuma Liberia, bayan da gwamnatocin kasashen suka tsuke bakin aljihunsu.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa "hakan ne kuma ya sa kasashen suka kasa daukan ma'aikatan kiwon lafiya."

Sai dai wani mai magana da yawun hukumar ta IMF, ya musanta wannan zargi, inda ya ce babu alaka tsakanin yaduwar cutar ta Ebola a kasashen da tsare-tsaren hukumar.