PDP ta sa 'yan Najeriya sun zama attajirai - Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan ya ce PDP ta sa an samu manyan attajirai

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce jam'iyyarsa ta PDP ta sa 'yan kasar da dama sun zama attajirai don haka ya kamata a ci gaba da zabenta.

Mr Jonathana ya ce, "wannan jam'iyyar, kamar yadda kuka sani, jam'iyya ce da ke bai wa 'yan kasuwa dama. Gwamnatocin da ke karkashin wannan jam'iyya na karfafa gwiwar masu zuba jari da kafa masana'antu".

A cewar shugaba Jonathan, a shekaru kusan 16 da jam'iyyar ta yi tana mulki, ta sa an samu manyan attajirai.

Mr Jonathan ya kara da cewa hakan ne ya sa yake so a sake zabensu.