Ana barazanar kuste a tashar nukiliya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi barazanar tafka aika-aika a lokacin Kirsimeti a tashoshin nukiliyar Korea ta Kudu

Kamfanin da ke lura da tashar makamshin nukiliya ta kasar Korea ta Kudu (KHNP) zai gudanar da gwaji don gano ko tashar tana da karfin kare kanta daga harin kutse ta intanet.

Wannan matakin ya biyo bayan fidda wasu bayanan tashar, da kuma fuskantar barazana daga wani mai kuste.

A cikin makon daya gabata, wani ko wata kungiya da ba a san ta ba, ta saki wasu bayanai da suka hada da taswirori da suka shafi tashar makamshin a intanet.

Kazalika, masu kutsen sun yi barazanar kara sakin dubban bayanan tashar makamashin.

Masu kutsen sun yi barazanar tafka aika-aika, inda suka nuna muddin ba a kashe wasu na'urorin sarrafa nukiliyar guda uku ba a lokacin Kirsimeti, to lallai mutane su nisance su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An fidda wasu bayanan sirri na tashar nukiliyar Korea ta Kudu a intanet

Sai dai kamfanin KHNP ya ce bayanan da aka saki a intanet ba su da hadari ga tsaron na'urorin.

Kamfanin na KHNP wanda shi kadai ne mallakin gwamnatin Korea ta Kudu mai tafiyar da nukiliya, ya na daya daga cikin ma'aikatun kasar masu samar da lantarki.

A cikin wata sanarwa, kamfanin KHNP ya ce zai gudanar da kasaitaccen aikin gwaji a manyan rassan tashar nukiliyar guda hudu.

Mahukuntan tashar makamashin sun ce an fara gudanar da bincike a game da fitar da bayanan sirri na tashar zuwa bainar jama'a.