An kama 'yan Afrika barayin motoci a Amurka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Irin wadannan motocin kasaitar barayin ke sace wa

Hukumomi a Amurka sun ce sun taka burki ga wani gungun barayin motoci 'yan Afrika ta Yamma a jihar New Jersey.

Gungun barayin yayi fashin motoci na alfarma kimanin guda dari da sittin, a titunan Amurka, ya kuma auna su a jiragen ruwa ya tura biranen Lagos da Accra, ta hanyar amfani da jabun takardu.

An kiyasta kudin motocin za su kai na dala miliyan tamanin.

A gabatar da tuhuma a kan mutanen su ashirin da shidda da suka hada da 'yan kasar Ghana hudu da wani dan Nigeria.

'Yan kasar Ghana su ne; Kojo Marfo da Standford Oduro da kuma dan Nigeria Ahmad Nasidi.