Mabiya Arsenal a Twitter sun kai 5m

Image caption Arsenal ce ta uku cikin kulob-kulob da suka fi mabiya a Twitter

Kulob din Arsenal ya zama kungiyar kwallon kafa ta gasar Premier ta farko da ta samu mabiya miliyan biyar a shafinta na Twitter.

Kazalika, kulob din shi ne na uku a cikin kungiyoyin kwallon kafa da suka fi yawan mabiya a Twitter.

Sauran kungiyoyin biyu su ne Real Madrid da Barcelona.

Richard Clarke shi ne editan shafin intanet na kulob din kuma ya ce, "Muna matukar farin cikin yadda muke bai wa magoya bayanmu a duk fadin duniya abubuwan da suke so".