Buhari ya bude shafukan sada zumunta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Buhari ya bude shafukan sada zumuntat ne domin ya tallata kansa

A Najeriya, dan takarar jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya bude shafukan sada zumunta da muhawara a yunkurin da yake yi na tallata kansa ga 'yan kasar.

Janar Buhari ya bude shafinsa na Facebook da Twitter da Instagram da YouTube.

A cikin kwana guda kadai da bude shafinsa na Twitter mai suna @ThisIsBuhari, dan takarar jam'iyyarta APC, ya samu mabiya fiye da dubu 27, yayin da shafinsa na Facebook mai suna Muhammadu Buhari ya samu wadanda ke "son" sa, wato "like" fiye da dubu153.

A sakonsa na farko da ya wallafa a Twitter, ya ce "Barkan ku da rana. Wanna shi ne shafina na Twitter da zan rika sada zumunta da ku".

Za a iya samun shafukan sada zumuntar nasa a shafinsa na intanet http://buhariforchange.com/

Shi ma Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP yana da shafin Facebook sannan kuma magoya bayansa sun bude shafukan goyon bayansa a Twitter.