'Yan kwadago sun soki gwamnonin PDP

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Jihar Plateau na cikin jihohin da suka gaza biyan albashi

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun soki gwamnonin jam'iyyar PDP saboda tarawa shugaba Jonathan kudin yin kamfe duk da cewa sun gaza biyan albashi.

A taron da jam'iyyar ta PDP ta gudanar a makon jiya, jiga-jiganta da suka hada da 'yan kasuwa da gwamnoni da sauran masu ruwa-da-tsaki a cikinta sun tara fiye da biliyon 21 don bai wa shugaban kasa ya yi kamfe da kuma gina Sakatariyar jam'iyyar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da akasarin gwamnonin da suka ba da gudunmawar suka kasa biyan albashin ma'aikata saboda a cewarsu, ba su da kudi.

Gwamnonin da ba su biya albashin ba sun hada da na Bauchi da Benue da Plateau da Akwa Ibom.

Shugaban kungiyar kwadago ta jihar Plateau, Comrade Jibrin Kwanga-Banchir ya ce tarawa PDP wadannan kudade kamar cin amanar kasa ne, yana mai cewa watanni fiye da hudu kenan da gwamnatin jihar ta ki bai wa ma'aikata albashi.

Sai dai kakakin gwamnan Plateau, Pam Ayuba ya kare matakin na gwamnoni, yana mai cewa batun tarawa jam'iyya kudi dana biyan albashi ba su da alaka.