Ukraine na shirin shiga kungiyar NATO

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rasha ta ce matakin ba alheri bane

Majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri'ar soke matsayin kasar na 'yar ba ruwanmu, domin fara daukar matakan shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce wannan mataki ba zai haifar da alheri ba, kuma zai haddasa zaman fargaba.

Sai dai ana cewa abu ne mai wuya Ukraine ta iya shiga kungiyar ta NATO a nan kusa, kuma kafin ta iya shiga sai ta sake kwato yankunan kasarta da yanzu suke karkashin 'yan a ware masu goyon bayan Rasha.

A yanzu haka, wasu yankunan gabashin kasar na karkashin ikon 'yan a ware kuma magoya bayan Rasha, yayin da Crimea kuma ta balle ta koma karkashin Rashar.