'Yansanda a Amurka sun kare harbe wani matashi

Masu zanga zanga a St Loius Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a St Loius

Mahukunta a Unguwar bayan birnin St Louis sun kare matakin wani dansanda farar fata wanda ya harbe wani matashi har lahira a kusa da wurin da aka yi harbin kisa a cikin watan Ogusta wanda ya haddasa bore na kwanaki.

'Yansanda a Berkeley sun shedawa manema labarai cewar wani saurayi mai shekaru 18, Antonio Martin, ya nuna wa jami'in dansandar wata bindigar dake dauke da harsasai.

Sai dai mahaifiyar mutumin da ya rasu ta musanta cewar danta na da bindiga:

Shugaban yansandan,Jon Belmar, ya ce abunda bai dace ne ba a nema cewar dan sandan yayi amfani da na'urar sa wanda ake zargi natsuwa da kuma bindigar harsashen roba a lokacin da suke tinkarar wadanda ake zargi dake dauke da makami.