Ban Ki-Moon ya yaba da kudurin makamai

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ban Ki-Moon ya yi fatan kudurin zai hana makamai fadawa hannun 'yan ta'adda

An fara aiki da wani kuduri na kasa da kasa akan kula da sayar da makamai, abinda ya samu yabawa daga babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

Mista Ban Ki-Moon ya ce yana fatan kudurin zai taimaka wajen hana makamai shiga hannayen masu take hakkin dan'adam, da 'yan ta'adda.

Manufar kudurin Majalisar Dinkin Duniyan kan cinikin makamai ita ce a rika gudanar da hada-hadar ta dala biliyan 85 bisa ka'ida.

Kasashe 130 ne suka rattaba hannu a kan kudurin, amma kasa da rabin kasashen ne suka jaddada aiki da shi, da suka hada da Amurka.

Kasashen Rasha da China sun ki sanya hannu a kanshi, yayin da kasashen Syria, da Iran da Korea ta Arewa suka kada kuri'ar rashin amincewa da shi.