Karatu ta kwanfutar hannu na da illa

Ipad Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwararrun sun gano illar da ke tattare da karatu da na'ura mai haske kafin kwanciya bacci.

Wani bincike da kwararrun likitoci suka gudanar, ya gano cewar karatu ta hanyar amfani da na'urar kwamfuta ta hannu, ko wayoyin komai da ruwanka na da matukar illa ga lafiyar bil'adama.

Kungiyar likitocin jamai'ar Harvard ta Amurka sun kwatanta karanta littafi mai shafi-shafi da kuma na na'urarr kwamfuta, inda suka gano illar da hasken na'urar zai yi ga lafiyar dan adam.

Binciken ya kuma gano cewa, wanda ya ke karatu da littafi mai shafi-shafi da daddare ba ya takurawa jikinsa sosai, kamar yadda mai karatu da na'ura yake yi ga kuma babbar illar da shi kansa hasken na'urar ke janyowa dan adam.

Haka ba zai samu bacci mai nutsuwa ba, idan kuma gari ya waye, wanda ya yi karatu da na'ura zai tashi jikinsa na masa ciwo, kuma a gajiye kamar wanda ya yi wani aikin karfi.

A dan haka kwararrun likitocin sun shawarci mutane da su rage karatu da na'ura mai haske, haka kuma su guje shiga wuri mai matukar haske da yammaci.

Sai dai a wani bangaren, an nuna damuwa kan hadarin da ke cikin zama a wuri mai tsananin haske kafin lokacin kwanciya bacci.

Dan haka kwararru sun bada shawarar yin amfani da fitilar da baat da tsanain haske da daddare, musamman kafin lokacin kwanciya bacci.

Kana kuma a rage yawan karanta littattafan da ake zubawa a cikin na'urorin kwamfuta irin su ipad, da iphone da sauransu.