Yaki da cutar Ebola zai iya faskara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce cutar Ebola zata cigaba da yaduwa a Afrika

Shugaban kwamitin yaki da cutar Ebola na Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce mai yiwuwa, cutar Ebola ta cigaba da yaduwa a yammacin Afrika na tsawon lokaci.

Farfesa Peter Piot ya ce mawuyaci ne a iya magance cutar kwata-kwata a cikin shekara daya.

Ya shaida wa BBC hakan ne bayan ya dawo daga kasar Saliyo, inda ya ce ya samu kwarin gwiwa da jin alkawarin samar da sabbin magungunan cutar wadanda ya yi amanna zasu samu a cikin watanni 3.

Cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 7500, akasarinsu a yammacin Afrika, kuma a 'yan kwanakin nan, kasar Saliyo, ta shiga gaban Laberiya a yawan masu kamuwa da cutar.