Sabon rikici ya barke a St Louis na Amurka

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Matasa sun fusata saboda ayyukan 'yan sanda a Amurka

An kara samun wani tashin hankali a birnin St Louis na Amurka bayan da wani dan sanda ya harbe wani matashi bakar fata.

An dai yi mummunan artabu tsakanin 'yan sanda da matasan da suka fusata yayinda labarin ya watsu cewar an kashe saurayin mai shekaru 18, a yankin da ake kira Antonio Martin a wani gidan mai.

Hukumar 'Yan sanda ta ce jami'in ya yi harbin ne domin kare kansa bayan da wanda ake zargi ya nuna shi da bindiga.

Harbin na baya bayan nan ya faru ne a Unguwar Berkely ta St Louis din, mai nisan kilomita uku daga Ferguson, Missouri inda wani dan sanda farar fata ya harbe har lahira, wani dan shekara 18 din, Michael Brown a cikin watan Agusta.

Mr Brown dai baya dauke da ko tsinke.