An sanya fim din The Interview a intanet

Image caption A kasar Amurka ne kadai ake iya samun fim din The Interview yanzu

Kamfanin shirya fina finai na Sony Pictures ya sanya fim din nan da ya janyo cece-kuce "The Interview" a intanet, bayan harin kuste da kamfanin ya fuskanta.

An sanya fin din ne a wasu zababbaun shafukan intanet da suka hada da "seetheinterview.com" da YouYube da Play, da kuma hanyar kallon bidiyo ta Xbox na Microsoft, amma har yanzu a Amurka ne kadai ake iya samun shi.

Ga masu sha'wan yin hayan fim din, zasu biya kudi dala 5.99, masu son su siya kuwa, zasu biya dala 14.99.

A baya kamfanin Sony ya dakatar da nuna fim din, wanda a ciki aka nuna wata makarkashiya ta kashe shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong-un.

Shugaban Amurka Barrack Obama ya soki kamfanin na Sony bisa dakatar da nuna fim din da ya yi.

Tun daga wancan lokaci, daruruwan gidajen sinima masu zaman kansu a Amurka sun nuna sha'awar nuna fim din.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana fim din The Interview a matsayin cin mutuncin kasarsa

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un da iyalan sojojin kasar sun bayyana fim din a matsayin cin mutuncin gwamnatin kasar.

Bayan an saki fim din a intanet, jama'a da yawa sun kasa shiga shafin "seetheinterview.com" domin su kalla saboda an yi wa shafin yawa.

Kamfanin Sony Pictures ya gamu da matsalar kutse da bai taba ganin irin taba daga wata kungiya mai kiran kanta Guardians Peace.

A cikin makon daya gabata, hukumar bincike ta FBI ta ce binciken data gudanar ya nuna kasar Korea ce ke da alhakin kutsen na baya bayan nan.

Sai dai wasu kwararru a fannin tsaron intanet sun musanta wannan zargi.