China ta haramta bikin Kirismeti

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An fi son mutane su bi al'adun China

Kafofin yada labarai a China sun ce hukumomi a yankin kudu maso gabashin kasar sun haramtawa makarantu gudanar da bukukuwan da suka jibanci Kirismeti.

Mahukunta a birnin Wenzhou sun ce a maimakon Kirismeti, ya kamata makarantu su maida hankali wajen bukukuwan al'adun China.

A farkon wannan shekarar, hukumomin birnin sun ba da umurnin a rusa majami'un da aka kafa ba bisa ka'ida ba, inda rahotanni suka ce an rusa gine-gine da dama.

A birnin Xi'an da ke tsakiyar China, an umurci dalibai su halarci wani dandali domin kallon wani fin da ke yi wa gwamnati farfaganda.

An kuma shawarci daliban su daina bin tsarin hutun da ake bi a yammacin duniya.