Wani matashi ya ci zarafin shugaba Erdogan

Shugaba Erdogan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnatin Mr Erdogan na fuskantar suka, daga 'yan adawar kasar.

'Yan sanda a kasar Turkiyya sun cafke wani yaro dan makarantar gaba da Firamare mai shekaru 17, da laifin cin zarafin shugaba Racep Tayyip Erdogan.

Wakilin BBC yace Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito, an tasa keyar matashin ne bayan ya zargi Mr Erdogan da jam'iyyarsa ta AK da cin hanci da rashawa a wani jawabi lokacin rangadi a tsakiyar birnin Anatolia.

Prime Ministan kasar Ahmet Davotugli ya kare matakin da jami;an tsaro suka dauka yana mai cewa dole ne a mutunta ofishin shugaban kasar.

Cin zarafin shugaban kasa dai babban laifi ne a kundin dokokin shari'ar Turkiyyar, kuma idan har aka samu dalibin da laifi zai fuskanci shekaru 4 a gidan kaso.