Za a kafa kotunan sojoji a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaiministan Sharif ya ce gwamnati zata yanke hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi

Firayiministan Pakistan ya ce za a kafa kotunan sojoji a kasar domin gudanar da shari'ar wadanda ake zargi da aikata ta'addanci cikin hanzari.

Mista Nawaz Sharif ya sanarda karin matakai na magance ayyukan 'yan bindiga a kasar, mako daya bayan 'yan kungiyar Taliban sun kashe fiye da yara 140 a wata makaranta a PeshAwar.

Firayiministan ya ce harin da 'yan kungiyar Taliban suka kai a Peshawar ya girgiza kasar sosai, a saboda hake ake da bukatar tsauraran matakai na kawar da tsatstsaurar akida a kasar.

Ya ce a baya, 'yan ta'adda suna guduwa batare da an hukunta su ba saboda tsarin shari'a mai rauni.

Kafa Kotunan sojojin wani bangare ne na sabbin matakan yaki da ta'addanci, da suka hada da hana 'yan ta'adda bayyana a kafafen yada labarai.