Kirisimeti: Sarauniya Izzabel za ta yabi masu agaji na Ebola

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarauniyar na gabatar da jawabin Kiristimetin ne a duk shekara

A jawabin da za ta gabatar na Kirisimeti, Sarauniya Izzabel ta Biritaniya za ta jinjina wa wadanda suke taimakawa wajen kokarin magance annobar Ebola.

Sarauniyar za ta yabi ma'aikatan agaji da ma'aikatan sa kai na lafiya da ta bayyana a matsayin wadanda suka sadaukar da kansu ta hanyar zuwa yammacin Afrika domin su taimaki masu fama da cuccuka kamar Ebola.

Ana sa ran Sarauniyar za ta yi jawabin ne da misalin karfe uku agogon GMT, wato karfe hudu agogon Najeriya da Nijar a ranar Alhamis.

Sakon Kiristimetin na Sarauniya wanda ke kunshe da ra'ayoyinta zai kuma yaba wa wadanda suka taimaka da kayan agaji ga mutanen da yaki ya daidaita.