An soki shirin korar daliban kimiyya a Burtaniya

Britain Students Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Masana sun ce lamarin zai zubar da kimar jami'oi Burtaniya a idon duniya

Masana kimiyya a Burtaniya sun soki shirin maida daliban kimiyyan 'yan kasashen waje gida bayan kammala karatun su.

Yanzu haka shirin wanda ake kokarin fara aiwatar da shi daga ofishin Sakatariyar cikin gida Theresa May ya janyo cecekuce a Burtaniyan.

Shirin wanda ya samu goyon bayan Sakatariyar na so ne ya dinga aikewa da daliban kimiyya zuwa kasashen waje zuwa gida da zaran sun kammala karatunsu.

Hakan ya sabawa tsarin da aka saba a baya na barin daliban su zauna na tsawon watanni hudu bayan sun kammala karatun domin su nemi aikin yi.

Koda yake tsarin ya amince da cewa masu kwazo daga cikin daliban kimiyyan 'yan kasashen waje za su iya neman aiki a Burtaniyan amma sai sun koma kasashensu da farko tukuna.

Sai dai masana kimiyya sun ce tsarin ya sabawa aniyar da gwamnati ta dauka a makon da ya gabata na maida hankali wajen ilimin kimiyya a kasar.

Darektar kungiyar nan mai rajin kare ilimin kimiyya a Burtaniya, Dr Sarah Main ta nuna takacinta ganin cewa tsarin zai kori masana kimiyya daga kasar.

"Barin daliban da muka koyar shiga ayyukan bincike na 'yan wasu shekaru zai taimakawa kasarmu matuka." In ji Dr. Main.