Daliban Chibok za su fara karatu a Amurka

Image caption An dauki nauyin karatun wasu 'yan matan Chibok a Amurka

A Najeriya, wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun kungiyar Boko Haram sun isa Amurka domin cigaba da karatunsu.

Kimanin dalibai 50 daga cikin 276 ne suka kubuta, bayan wasun su sun shafe kwanaki 3 acikin dajin Sambisa a hannun kungiyar.

Daliban zasu yi shekaru biyu a sabuwar makarantarsu a Amurka, inda zasu kammala karatunsu wanda kungiyar Boko Haram taso ta haramta musu.

'Yan matan sun yi farin cikin yin Kirsimeti a Amurka, sabanin a bara lokacin da suka yi ta cikin fagabar Boko Haram.

Har yanzu, akwai fiye da daliban 200 da ke hannun kungiyar.