Katsina: Masari na fuskantar kalubale

Nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masari ya musanta zargin

Bayan da ya lashe zaben fidda gwani a karkashin jam'iyar APC a matsayin dan takarar gwamna a jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari na fuskantar kalubale.

Dan takarar da ya zo na biyu a zaben, Sanata Kanti Bello na zargin cewa tsohon Kakakin majalisar wakilan kasar, Masari na amfani ne da takardar karatu ta bogi.

Hakan kuma ya sa ya ce bai amince da kayen da ya sha ba inda ya nemi da a gudanar da bincike.

Sanata Bello har ila yau ya zargi jam'iyar ta APC da yin biris da lamarin.

"Kamin a yi zaben an yi kuka ba a yi komai ba, aka zo wajen tantancewa aka yi kukan ba a yi komai ba." Inji Sanata Kanti Bello.

Sai dai jam'iyar ta yi watsi da zargin da yake yi yayin da shi ma Alhaji Masari ya yi watsi da lamarin inda ya ce kage ne kawai Sanata Bello ya ke yi.

"Karya ce, na kuma ce karya ce kuma a shirye nake daga nan ko zuwa kololuwar sama ne in kare wannan abu." Inji Masari.