Ana musayar fursunonin yakin Ukraine

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mahaifiyar daya daga cikin sojojin Ukraine da aka sako ke nan ta rungume shi

A kasar Ukraine an yi musayar daruruwan fursunonin yaki daga bangarorin magoya bayan Rasha da na dakarun kasar da ke fafatawa da juna.

Wannan wani mataki ne na sabunta yunkurin da ake yi na aiwatar da shirin zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu da aka cinma a baya.

Akalla sojojin Ukraine 146 aka sako da yammacin Juma'a yayin da kuma ake jira a sako wasu sojojin hudu.

A nata bangaren, ana sa ran kasar ta Ukraine za ta sako fursunoni kusan 220 wadanda ke goyon bayan Rasha ko kuma 'yan aware.

Wakilin BBC ya ce "wannan wani lamari ne da za a zura ido a gani ko hakan wata alama ce da za ta nuna cewa za a samu biyan bukata a rikicin."

Sai dai rahotanni sun ce an kasa cimma yunkurin rattaba hannu a kan sauran matakan samar da zaman lafiya, bayan da gwamnatin Ukraine ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa zuwa yankin Crimea da Rasha ta karbe a watan Maris.