Matsala a shafukan Xbox da PlayStation

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marikar buga wassanin Xbox

Shafukan intanet na wasannin kwamfuta na Xbox da PlayStation sun fuskanci matsala, yayin da ake zargin wata kungiyar masu kutse da haddasa matsalar.

Kamfanonin Microsoft da Sony wadanda ke kirkirar wasannin kwamfuta sun shaida wa masu mu'amala da su cewa suna sane da matsalar.

Wata kungiyar masu kutse mai suna "Lizard Squad" ta yi ikirarin haddasa matsalar.

Kamfanonin Sony da Microsoft basu ce komai ba agame da ikirarin kungiyar Lizard Squad, sai dai sun tabbatar da cewa suna kokarin magance ta.

Wata mata, Ros Bruce ta ce yaronta mai shekaru 10 ya sayi Xbox One domin ya buga wasanni lokacin kirsimeti tare da abokinsa.

Ta ce yaron ya dauki lokaci mai tsawo yana kokarin sauke wasannin da yake so daga intanet amma abin ya faskara.

Ta ce "yaro na ya wuni ya na kuka saboda yakasa sauke wasannin da yake so".

"Ina ganin kamfanin Xbox zai biya mu diyya" Ros Bruce ta ce.