Wani jirgin sama na Malaysia ya bace

Image caption Wasu jami'ai na ganin kila mai ya kare wa jirgin ne

Kamfanin jirgin saman AirAsia da ke Malaysia ya ce ya kaddamar da aikin neman wani jirginsa da ya bata, kusan minti 45 bayan da ya tashi daga birnin Surabay na Indonesia zuwa Singapore.

Sama da mutane 160 ke cikin jirgin (Airbus 320), yawancinsu 'yan kasar Indonesia ne.

Kamfanin na AirAsia ya ce an kasa smun sadarwa da jirgin mintina 45 bayan da ya tashi daga birnin Surabayan.

Wani kakakin ma'aikatar sufurin jiragen saman Indonesia ya ce an kasa tuntubar jirgin ne a tsakanin tsibiran Kalimantan da Java.

Jami'in ya ce da farko matukin jirgin ya yi waya inda ya bukaci a duba masa wata hanya da zai bi da jirgin, amma ba a san dalilin da ya bukaci hakan ba.

Sai dai an ruwaito wasu jami'an Indonesia na cewa yanayi a yankin ba shi da kyau.

kamfanin jirgin ya samar da wata cibiyar wayar gaggawa domin amsa kiran iyalai da 'yan uwan wadanda ke cikin jirgin.

A shekaran nan kamfanin jirgin sama na kasar Malaysia, wato Malaysia Airlines ya yi asarar jiragensa biyu, amma wannan kamfanin na AirAsia bai taba rasa jirginsa ta wani hadari ba.