Jirgin AirAsia ya bace da mutane 162

Hakkin mallakar hoto epa

Ana zaman zullumi a Indonesia bayan bacewar wani jirgi da ya tashi daga birnin Surabaya na kasar zuwa Singapore.

Jirgin, kirar Airbus 3-20, na dauke ne da mutane 162, cikin su harda mata da yara kanana.

Indonesia da Singapore sun tura jirage domin cigiyar sa.

Sai dai an dakatar da aikin neman jirgin saboda dare ya yi a yankin da ya bace.

An daina jin duriyar jirgin ne sa'o'i kadan bayan tashin sa.

Matukin jirgin ya nemi iznin karkatar da akalar jirgin, kuma daga nan sai sadarwa ta katse tsakanin sa jami'an filin jirgin saman Surabaya din.

Sean Maffet, wani tsohon sojan saman Birtaniya ya shaidawa BBC cewa: "Akwai mummunan yanayi a wurin da jirgin ya bace. Ina ganin za a iya cewa matsalar ce ta sa matukin jirgin ya bukaci ya karkatar da akalar jirgin. Babu mamaki ya ga bakin hadiri ne kuma ya yi kokarin kauce masa."

Mataimakin shugaban Indonesia Jusuf Kalla, ya shaidawa manena labaru cewa watakila jirgin "ya yi hadari ne".