An koma aikin neman jirgin AirAsia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nan da sa'oi kadan ne za a koma neman jirgin

Jiragen saman kasar Indonesia da wasu jiragen ruwa na soji da dama hade da wasu na Malaysia da na Singapore ne suke gudanar da aikin.

Kasar Australia ma ta aike da jirgin sama guda domin taimakawa.

A ranar lahadin da ta gabata aka kaddamar da aikin sai dai an dakatar saboda dare ya yi a yankin da jirgin ya bace.

Jirgin, kirar Airbus 3-20, na dauke ne da mutane 162, cikin su harda mata da yara kanana.

An daina jin duriyar jirgin ne sa'o'i kadan bayan tashin sa.

Matukin jirgin ya nemi iznin karkatar da akalar jirgin, kuma daga nan sai sadarwa ta katse tsakaninsa jami'an filin jirgin saman Surabaya din.

Mataimakin shugaban Indonesia Jusuf Kalla, ya shaida wa manena labaru cewa watakila jirgin "ya yi hadari ne".

Yanzu haka ana zaman zullumi a Indonesia bayan bacewar jirgin wanda ya tashi daga birnin Surabaya na kasar zuwa Singapore.