Ministan tsaro na Faransa zai zo Africa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A 2013 Le Driant ya yi bikin sabuwar shekara a garin Gao na Mali inda 'yan jihadi suka kafa sansanoninsu.

Ministan tsaro na Faransa, Jean Yves Le Driant, zai kai wata ziyara a sassan nahiyar Afrika da mayakan sa kai suka addaba.

Ministan zai kai ziyarar ne a kasashe kamar su Mali da Chadi da kuma Nijar, masu fama da masu tayar da kayar baya.

Ministan na nuna fargaba kan yadda mayakan da'awar Jihadi da aka kora daga Mali suka tattaru a Libya.

Yana ganin hakan zai iya sa al'amura su tabarbare a Libyan.

A kan hakan ne ministan yake ganin ya kamata a 2015 kungiyar kasashen Africa da Majalisar dinkin duniya da kasashe makwabtan Libya su mayar da hankali kan harkar tsaro.

A shekarar 2013 ne dai Le Driant ya gudanar da bikin sabuwar shekara a garin Gao na kasar Mali inda 'yan jihadi suka kafa sansanonin su.