George Weah ya lashe kujerar majalisar dattawa

George Weah Hakkin mallakar hoto
Image caption Goerge Weah ya kayar da dan shugabar kasar Robert Sirleaf

Tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Liberia, George Weah, ya lashe zaben kujerar majalisar dattawan mazabarsa.

A makon da ya gabata ne aka gudanar da zaben.

Mr. Weah ya samu kashi 78 na kuri'un da aka kada a mazabar Montserrado da ta hada har da birnin Monrovia.

Abokin hamayyarsa Robert Sirleaf, wato dan shugabar kasar Ellen Jonhson Sirleaf, ya samu kusan kashi 11 na kuri'un.

Har ila yau sauran wadanda suka samu nasara a zabukan 'yan majalisun akwai tsohuwar matar tsohon shugaban kasar Liberian Charles Taylor dake tsare.