Babu sabani tsakanin Nigeria da Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nigeria na fafutukar sayo makamai daga kasashen duniya, don yaki da 'yan Boko Haram

Jakadan Nigeria a Saudi Arabia ya ce ba rashin jituwa ba ne ya sa Saudiyyan ta hana wani jirgi da ke dauke da makaman da Nigeria ta sayo daga Pakistan wucewa ta sararin samaniyarta ba.

Jakada Abubakar Shehu Bunu ya gayawa BBC cewa, hukumomin Saudiyyan sun ce a ka'ida kamfanin jirgin saman ne ya kamata ya nemi izinin wucewa ta kasar tun da ba jirgi ne na gwamnati ba.

Ya kara da cewa idan da jirgin na gwamnatin Nigeria ne to da ba a hana shi wucewa ba, sabo da ba su da mtsala da Saudiyyan.

A ranar Litinin ne wasu kafofin yada labarai a Nigeria suka ba da rahoton cewa rashin ba da iznin wucewa da makaman da Nigeria ta sayo domin yaki da 'yan Boko Haram, alama ce ta tsamin dangantaka tsakanin kasashen.

Jakadan ya bayar da misalan wasu ayyuka na cigaban kasa da ya ce bankin raya Islama na Saudiyyan na yi a Nigeria a matsayin alamar kyakkyawar dantaka tsakaninsu.