Ba Jonathan ne ke sa ta'addanci ba - Minista

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren da Boko Haram ke kai wa a arewacin kasar sun yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Ministan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Bala Mohammed ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hannu a hare-haren ta'addancin da ake kai wa a arewacin kasar.

Ministan ya bayyana haka ne a Bauchi , lokacin da tawagar gwamnati ta je garin domin yin jaje da kai wa mutanen da hare-haren da aka kai a kasuwar Bauchi suka shafa.

Bala Mohammae ya ce, "duk lokacin da ta'addanci ya shiga kasa yana da wahalar fita. Gwamnatin tarayya ba ita take yin wannan (ta'addanci) ba; kuma gwamnati so take a samu masalaha".

Tawagar gwamnatin tarayyar dai ya kai wa mutanen da hare-haren suka shafa kayayyaki da dama domin share musu hawayensu.

Hare-haren da aka kai a kasuwar ta Bauchi sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.