Boko Haram ta 'bulla' a Ghana

Boko Haram ta kashe dubban mutane

Asalin hoton, AFP BOKO HARAM

Bayanan hoto,

Boko Haram ta kashe dubban mutane

A Ghana, rundunar 'yan sandan jihar gabashin kasar ta umurci shugabannin al'ummar Musulmin zangon garin Akim Ofoase dake jihar da su rusa wata kungiyar sintiri da suka kafa da ake kira Boko Haram saboda aikace aikacen kungiyar sun saba ma doka.

A wata sanarwa da ta fitar hukumar 'yan sandan ta ce shugabannin Musulmin sun kafa kungiyar ce don ladabtar da yaran Zangon da suka ce suna shashanci maimakon zuwa makaranta.

Ana dai zargin kungiyar da yi wa mutane bulala da kuma hana su ciniki da mabiya addinin Krista, zargin da suka musunta.

Kungiyar ta Boko Haram, wacce ke da mazauni a Najeriya, ta tsallaka zuwa kasar Kamaru.