Jiragen Kamaru sun hallaka 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen Kamaru sun kai wa 'yan Boko Haram hari

A karon farko, dakarun kasar Kamaru sun kai wa 'yan Boko Haram hari da jiragen sama.

A karshen makon jiya ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a kauyuka da garuruwa da dama na Kamru.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya ce an hallaka fiye da mutane 30 lokacin da aka kai harin.

Kazalika, rahotanni sun ce sojin Kamaru sun gudu daga barikinsu bayan 'yan Boko Haram sun kai masa hari; sai dai sun kwato shi daga baya.