Zabe kafin cikar wa'adi a kasar Girka.

Firayim ministan Girka Antonis Samaras Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Firayim ministan Girka Antonis Samaras

Jagoran jam'iyar Syriza mafi farin jini (Alexis Tsipras),ya yi alkawarin cewa matsin tattalin arziki zai zama tarihi a kasar, muddin jam'iyarsa ta samu galaba a zaben.

Ministan harkokin kudi na kasar Jamus Wolfgang Schaeuble yayi gargadin cewa babu wani zabi ga hanyoyin yin garanbawul a kasar.

Basukan gwamnatin kasar ta Girka sun karu da kashi 9 cikin dari, alamun da ke nuna cewa masu zuba jari basu da tabbaci game da makomar tattalin arzikin kasar.