An kubutar da fasinjojin jirgin ruwa a Italiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin ya kama da wuta a cikin teku

Dakarun da ke tsaron gabar tekun Italiya sun ce a yanzu an kubutar da daukacin fasinjojin da ke cikin wani jirgin ruwa da ke cin wuta a tekun Adriatic.

Fira ministan Italiya, Matteo Renzi ya ce tabas an tserad da fasinjojin su dari hudu da bakwai.

Mutane biyar ne dai ka tabbatar da sun mutu sakamakon lamarin.

Jirage masu saukar angulu ne suka yi ta jigilar daruruwan mutane zuwa tudun mun tsira yayin da jami'an kashe gobara ke ta kokarin shawo kan gobarar.