INEC ta sauya wa kwamishinoninta wurin aiki

Hakkin mallakar hoto b
Image caption INEC na fuskantar kalubale kan zabukan 2015

Hukumar zaben Nigeria-INEC ta sauya wa duka kwamishinoninta wurin aiki a wani mataki na shirye-shiryen zaben shekara ta 2015.

Sakatariyar INEC, Mrs. Augusta Ogakwu a wata sanarwa ta bayyana sauya wa kwamishinonin jihohin su 37 wurin aiki zuwa wasu jihohin na daban.

Galibin kwamishinonin su ne suka lura da zabukan da aka yi a kasar a shekara ta 2011.

Wannan sauyin bai rasa nasaba da kokarin hukumar zaben domin tabbatarda cewa kwamishinonin da suka dade a wasu jihohi ba za a yi amfani da su ba wajen aikata abubuwan da basu dace ba a lokacin zabe.

Sanarwar ta umurci kwamishinonin su kamalla shirye-shirye mika takardun sauya wurin aiki zuwa ranar 31 ga watan Disamba.